*195 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*MENE NE HUKUNCIN SHAN MAGANIN QARA QIBA?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Malam mene hukuncin mutanen da ke shan tablets wadanda suke sa su qiba?
Duk dacewa akwai wadanda suke rasa qiba ko girma nawani bangare na jikinsu as a result of their hormones doe's not work properly. Idan suka ga doctor ana ba su tablet kuma hormone din ya cigaba da aiki yadda ya kamata, kuma za su yi qiba, kuma gurin da baya girma a jikinsu zai cigaba da growing.AMSA:
Wa'alaikumus salam, hukuncin Shan maganin qara qiba ya kasu gida biyu:
1. Duk wanda ya sha maganin qara qiba ta dalilin wani rashin lafiya da ke hana garkuwan jikinsa haɓaka da girma, to wannan babu laifi saboda wannan lallurar, domin shi wannan rashin qibar tasa ta cuta ce, kuma neman magani halas ne a addini.
2. Duk wanda kuwa ya sha maganin qara qiba haka kurum ba don wata matsala mai sa rama da ke buqatar yin hakan a Likitance ba, kawai ya yi haka ne don ya qara girman jikin da Allah ya ba shi, saboda ya qyara kyau ko kwarjini, to wannan ya canja halittar Allah, kuma canja halittar Allah haramun ne kamar yadda nassoshin Shari'a suka tabbatar.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
2/12/1440 h.
03/08/2019 m.

YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: