*Tambaya ta 117*
*ZUBAR DA CIKIN DA BAI FARA MOTSI BA*
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.
Meye hukuncin matar da ta zubar da cikin da bai fara motsi ba, saboda tsoron zai wahalar da ita, kuma don jaririn da take shayarwa?AMSA A117:
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
A cikin amsar tambaya ta A026 da ya gabata mun yi bayanin cewa: Haihuwa ni’ima ce. Muka ce:
[2] Ni’imomin da Ubangiji Ta’aala ya yi wa bayinsa a koyaushe suna da yawan gaske, kamar yadda ya faɗa a cikin Suratun Nahl:
وَإِنْ تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللَّهِ لَا تُحْصُوهَا إِنَّ اللَّهَ لَغَفُورٌ رَحِيمٌ
Kuma in da za ku lissafe ni’imomin Allaah a gare ku, ba za ku iya ƙididdige su ba, lallai Allaah tabbas! Mai Yawan Gafara ne, Mai Yawan Rahama.Sai dai kuma duk da hakan ba mu taɓa ko jin labarin wani mutum guda ɗaya mai hankali da tunani ba ya taɓa ƙyamatar ko da mafi ƙanƙantar baiwa guda daga cikin ɗimbin ni’imomin Ubangiji Ta’aala ba a gare shi. Babu wanda ya taɓa ƙyama ko jin haushi idan itatuwan mangwaro ko lemu ko ayaba a gonarsa suka fitar da ’ya’ya masu yawan da bai taɓa ganin irinsu ba. Haka kuma ba wanda ya taɓa nuna baƙin cikinsa ko ɓacin ransa a lokacin da shanunsa ko tumakinsa da awakinsa ko talo-talo ko agwagi da kajin da yake kiwo suka samu yawan albarkar ’ya’ya! Sannan kuma a iya saninmu da tarihin rayuwar al’ummomin duniya, ba a taɓa samun waɗansu mahankalta da suka nuna ƙyamatar yawan haihuwar ’ya’ya a cikin jama’arsu ba!
Har zuwa inda muka ce:
A taƙaice dai, babu wata hujja ko wani dalili na ƙyamar haihuwa ko ɗaukar matakan daƙile cigaba da halittar abin da ke cikin ciki tun kafin bayyanarsa a duniya. Allaahumma, sai dai in an tabbatar ko ana kyautata zaton aukuwar wata matsananciyar wahala mai kaiwa, wataƙila ga salwantan rayuwar mai haihuwar ko kuma abin da za a haifa, amma ba talauci ba! Domin a cikin Hadisin Sahabi Abdullah Bn Mas’uud wanda Al-Bukhaariy da Muslim suka fitar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya tabbatar mana da cewa, tun a lokacin da jaririn yake cikin cikin mahaifiyarsa ne aka gama rubuta arziƙinsa:
ثُمَّ يَبْعَثُ اللَّهُ مَلَكًا فَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ وَيُقَالُ لَهُ اكْتُبْ عَمَلَهُ وَرِزْقَهُ وَأَجَلَهُ وَشَقِيٌّ أَوْ سَعَيدٌ
Sai kuma Allaah ya aika masa da Mala’ika, sai kuma ya umurni da abubuwa huɗu, ya ce da shi: Rubuta irin aikinsa, da arziƙinsa, da ajalinsa, da kuma ko ɗan Wuta ne ko kuma ɗan Aljannah.
Wannan kenan.
Kuma yana da kyau mu san cewa: Ɗaukar matakan daƙile cigaba da halittar abin da ke cikin ciki tun kafin bayyanarsa a duniya shi ma yana da hatsari dangane da lafiyar jiki. Don haka, sai in ya zama dole sannan ake bin wannan hanyar.
Don haka, idan larura ce ta sanya mace zubar da cikin, to ba za a ce tana da laifi ba, musamman ma idan ya zama bai kai lokacin da aka riga aka busa masa rai ba. Watau idan bai kai girman watanni huɗu ba. Domin sai ya kai wannan lokacin ne, ake busa masa rai kuma a aika masa da mala’ika, kamar yadda bayanin hakan ya zo a cikin hadisin da ke sama. Wannan lokacin kuma shi ne ma’anar: Bai fara motsi ba, kamar yadda masana suka yi bayani.
Wal Laahu A’lam.*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
6/8/2019
7: 04am
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Storie brevi*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: