*AMSOSHIN TAMBAYOYIN KU*
*SHIN AZUMI YA WAJABA A KAN DAN SHEKARA 15?*
TAMBAYA:
Assalamu Alaikum, malam barka da azumi, da fatan Allah ya bamu ladansa, malam dan Allah ina son in san actual shekarun da namiji azumi ya wajaba a gare shi, muna da yaro yana cikin shekara ta 15 Amma muryar shi ta yi nauyi kuma gashin hamata ya fito mishi amma abun da ba mu sani ba ko ya yi mafarki, to shi ne bai son yin azumi ni kuma ina ganin kamar azumi ya wajaba a gare shi amma babanshi yana yi mishi daukar karamin yaro.
AMSA:
Wa'alaikumus Salam, Duk yaron da waɗannan abubuwa guda uku suka tabbata a tare da shi, to babu shakka ya kai haddin balaga:
1. Tsurowar gashin mara, ko na Hammata.
2. Kai wa shekara goma sha biyar.
3. Yin mafarki.Matuqar ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa uku ya sami yaro namiji, to ya balaga, kuma azumi da sauran ibadoji kamar sallah da sauransu, sun hau kansa. Idan kuma mace ce sai a qara mata da:
4. Al'ada ko Haila.
Dazarar ɗaya daga cikin huɗun nan ya tabbata ga ƴa mace, to itama azumi da sauran ibadoji sun wajaba a kanta.
Saboda haka, kuskure ne a bar yaron da ya kai shekara goma sha biyar (15), ko ya taɓa yin mafarkin saduwa, ko gasun mara da hamata suka fito masa ya qi yin azumi.Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
15/Ramadan/1440 h.
20/05/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Historia Corta*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: