*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

289 10 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN MACE ZA TA IYA YIN KARATUN ALQUR'ANI WANI SASHE NA JIKINTA A BUƊE SABODA ZAFI ALHALI MALA'IKU NA SAUKA A WURIN?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, malam Allah ya dada haske, don Allah yanzu lokacin zufa ne to ina karatun Qur'an babu dankwali a kaina kuma iya best ne a jikina shin babu matsala ganin cewa ance Mala'iku na sauka ga shi wani shashi na jikina ya bayyana?

AMSA:

Wa'alaikumus salam, Haqiqa ya tabbata a hadisi cewa Mala'iku suna sauka a wurin da ake karanta littafin Allah, kuma ba shi daga cikin sharaɗin karanta Alqur'ani ya zama mace sai ta rufe kanta, musamman a inda babu ajnabiyyi, amma dai yana daga cikin ladubba mutum ya suturce tsiraicinsa yadda ya dace, sai dai idan lalura ta samu a inda ba zai yiwu a sa sutura da za ta game jiki ba duka, to wannan ladabin babu laifi idan bai samu ba, saboda lallurar zafin yanayi da makamantan haka.

Kuma kasancewar Mala'iku na zuwa wurin ba shi ke nuna cewa za su kalli al'aurarki ba, saboda ai ko banɗaki mutum ya zaga wasu malaman suna da fahimtar cewa mala'ikun nan masu qidaya aiki suna nan tare da shi, wasu malaman kuma suna da fahimtar Mala'ikun suna kaucewa ne har sai mutum ya fito daga banɗakin, amma kuma hakan ba ya dakatar da su ga sanin abin da yake aikatawa.
Don haka, ko ma dai wanne ne daga cikin waɗannan fahimta na malamai, to dai Mala'iku suna sauka a inda ake karanta Alqur'anin, saboda su ai karatunki suke sauraro ba ke suke kallo ba.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
9/7/1440 h.
16/03/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now