AMSOSHIN TAMBAYOYINKU

1K 23 0
                                    

TAMBAYA 1,307
Assalamu alaikum.Malam Allah ya saka da alkhairi,ina da tambaya guda biyu(1) mutum ne ana binshi sallar azahar da la asar gashi kuma antada sallar magrib shin zai bi magrib ne ko ya zai yi. (2) malam mutum ne ya shigo masallaci sai ya tadda an idar da sallar magrib za a had a da isha to zai fara kawo magrib ce ko zaibi isha ko ya zai yi na gode.
AMSA
1. indai lokacin magariban yana da tsawo har zai iya yinsu dukka lokacin magariban bai fita ba to ya shiga sallar magariban da niyyar azahar idan sukayi raka uku akayi sallama sai ya tashi ya cikato ɗayan, sannan sai yayi la'asar bayanan yayi magariba anan an samu biyan bashi da kuma yinsu sallolin a jere wannan ana magana idan har yana da uzuri karɓaɓɓe a shari'a dayasa baiyi azahar da la'asar ba amma idan babu uzuri har lokacinsu ya fita sai dai yayi ta istigfari da kuma nafila amma ko yayi Allah bazai karɓa saoda kowacce Allah ya mata lokaci kamar yanda ya faɗa a cikin suratul Nisa'i.
2. Shima zai shiga isha'i ne da niyyar magariba idan anyi raka'a uku sai ya zauna yayi tahiya yayi sallama, idan har basu gama raka'ar ƙarshe ba sai ya shiga ya bisu isha kuma.
Wannan bayani na cikin fiqhul muslim na Abu Ammarul misri.
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib
TAMBAYA 1,308
Assalam Allah ya albarkaci rayuwar malam, tambayata anan shine idan mutum zai yi sallah da matarshi itace zatayi iqama ko shine.? Kuma idan ya Kai fatiha ya halatta tace ameen a bayyane, daga karshe idan zatayi sallar da ake bayyana karatu a fili ya kamata tayi karatun a bayyane ne ko ta boye.?
AMSA
Idan miji da mace zasuyi sallah shi zai tayar da iƙama don ita mace ba a buƙatar iƙama a wajenta saboda alama ce mai girma wanda ba a buƙata a wajen mace, sannan babu laifi idan yayi karatu a bayyane babu laifi don tace amin saboda tsakaninsu babu haramci sannan duk irin yanda namiji zaiyi sallah haka mace zatayi saboda annabi cewa yayi ((kuyi sallah kamar yanda kuka ga inayi)) anan bai ware mace daga namiji ba.
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now