*NA QI YARDA MIJINA YA SADU DA NI A ƊAKIN KISHIYATA A LOKACIN BA TA NAN, SHIN NA

165 5 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*NA QI YARDA MIJINA YA SADU DA NI A ƊAKIN KISHIYATA A LOKACIN BA TA NAN, SHIN NA YI LAIFI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, Malam ina da tambaya, mu biyu ne a gurin mijinmu, amma ba mu a tare kowa da garinsa, mukan yi wata uku ba mu hadu ba sai dai idan za a yi sha'ani tukunna mukan hadu da juna, to sai wata rana ni na tafi garin da kishiyar tawa take da watan azumi, kuma a lokacin mijin namu yana gurinta, to irin tana zuwa sallar Tahajjud da karfe dayan dare (1am), to a ranar ma ta tafi sallar, kuma ta tafi ta bar mu a dakinta muna kwance mu biyu da ni da mijina, sai bayan ta tafi sallah sai shi mijina ya nemi ya sadu da ni a gadonta amma sai na ki yarda, na ce ai wannan cin amana ne, to don Allah malam kin amincewan da na yi ina da laifi a gurin Allah? Saboda na roke shi ya yafe min idan na yi ba daidai ba, na gode.

AMSA:

Wa'alaikumus Salam, Allah ne mafi sanin dai-dai, amma ni a fahimtata kin yarda da kika yi bai dace ba, saboda kasancewar da yardarta ta tafi ta bar ku a ɗakin a kwance da ke da mijin naku, saboda ba sharaɗi ba ne sai a ɗakinki sannan zai iya kusantarki da mu'amalar aure, matuqar an sami kaiɗaituwar da ba wanda ya san abin da ke gudana a tsakanin ma'aurata, saboda haka nake fahimtar qin amincewarki da shi a matsayin kuskure. Duk da dai lamarin yana kunshe da shubhohi.

Ya tabbata a littafan hadisi da littafan Tafsiri cewa Annabi ﷺ ya kusanci baiwarsa Mariyatul Qibɗiyya a ɗakin Nana Hafsa a lokacin da ta tafi ziyartar iyayenta, sai Nana Hafsa da ta dawo ta same su a ɗakinta, ta dakata ba ta shiga ba, har sai da Mariya ta fito sai ta shiga ɗakin, da ta shiga sai ta ce wa Manzon Allah ﷺ ya Manzon Allah a ɗakin nawa, kuma a kan shimfiɗana?

Sai Annabi ﷺ bai ji daɗin haka ba, a qarshe ya haramta wa kansa kusantar Mariya, kuma ya ce kada ta faɗa wa Nana A'isha abin da ya faru, da kuma maganganun da ya faɗa mata, sai Nana Hafsa ta yi kuskure ta sirranta wa Nana A'isha abin da ya faru, da faruwar haka sai Allah ya saukar da suratut Tahreem, wanda a cikinta aka gargaɗi Nana A'isha da Nana Hafsa a kan wannan abu da ya faru, kuma aka goge haramcin da Annabi ﷺ ya yi wa kansa ba zai sake kusantar kuyangarsa Mariya ba...

Abin lura a wannan qissar shi ne ba a zargi Annabi ﷺ da abin da ya aikata na kusantar wancan baiwa tasa a ɗakin Nana Hafsa kuma a kan shimfiɗarta ba. Abin ma da Allah ya ce shi ne: Don me yake haramta wa kansa abin da Allah ya halasta masa? Duk da ba an ba da qofar yin hakan ba ne, amma wannan yana nuna cewa idan lalura ta sa za a iya yin hakan, sai dai barin hakan shi ya fi alheri musamman a irin zamantakewarmu na aure na wannan lokaci.

Domin samun cikakken bayanin sai a duba Tafseeeruɗ Ɗabariy ko Tafseerul Qurɗabiy, ko Tafseerul Qur'anil Azeem na Ibn Katseer a qarqashin surat Tahreem.

Ko a duba Almu'ujamul Ausaɗ na Aɗɗabarániy hadisi mai lamba ta 2316, ko Sunanud Dáruquɗniy hadisi mai lamba ta 4013.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
12/7/1440 h.
19/03/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now