*NA WANKE WA YARONA BAHAYA, YA MATSAYIN ALWALATA

93 1 1
                                    

*024 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*NA WANKE WA YARONA BAHAYA, YA MATSAYIN ALWALATA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Malam ni ce na yi alwala sai yarona ya yi bahaya, sai na wanke masa. Shin zan sake yin wata alwala ce koko zan iya sallah da ita?

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu. Ƴar uwa alwalarki tana nan, kuma za ki iya yin sallah da ita, abin da kawai za ki yi shi ne, bayan kin gama wanke wa yaron bahayar, sai ke ma ki sa hannunki a qasa ki wanke tare da qasar, ko kuma ki sa sabulu ko omo, ko wani sinadarin makamantansu. Saboda ai ba ke ce kika yi bahayar ba, kuma dama malaman Fiqhu sun kasa tsarki zuwa gida biyu ne, wato tsarkin hadasi da tsarkin khabasi, kuma dukkansu ibada ba ta inganta sai da su, kuma su ma ba sa inganta sai da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa.

1. TSARKIN HADASI (طهارة الحدث):
Abin da ake nufi da tsarkin hadasi shi ne tsarkake najasar da ke fita ta hanyoyin nan guda biyu, wato dubura da gaba (zakari ko farji), kamar fitsari da maziyyi da bahaya da sauransu.

2. TSARKIN KHABASI (طهارة الخبث):
Wannan kuma nau'i ne na tsarki da ya shafi tsarkake wurin sallah, da tufafin mai sallah, da darduma ko tabarma ko najasar da ta taɓi jikin mai sallah, da makamantan haka.

Wannan nau'in tsarki na biyun shi ne hukuncin wanda ta wanke wa yaronta bahaya bayan ta yi alwala, wato alwalarta tana nan, wanke hannun kawai za ta yi.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
26/4/1440 h.
02/01/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now