*ZAN IYA YIN WUTIRI BAYAN KETOWAR ALFIJIR ??*
*Tambaya*
Asslm alkm, malam inada tambaya, ko yana halatta in ranka wutri bayan ketowar alfijir, sannan wutri kashi nawa ne kuma yaya kaifiyyar su take?
*Amsa*
Wslm Wrhmtlh Wbrkth WUTIRI ana yinsane daga bayan isha'i zuwa kafin ketowar alfijir, don Hadisinda ANNABI SAW cikin ruwayar MUSLIM daga ABU SA'ID AL-KHUDRY yace👉🏼
أوتروا قبل أن تصبحوا
wato= kuyi wuturi kafin asubah,
Amma ga wanda yamakarane ko yamanta yana iyayi koda bayan ketowar Alfijir don hadisin ABU SA'AD ruwayar AS'HABUSSUNAN banda NASA'I, ANNABI SAW yace👉🏼
من نام عن الوتر أو نسيه فليصل إذا أصبح أو ذكره
Wato= wanda barci ko mantuwa yasa wutiri yasubuce masa- yayi koda asuba tayi,Amma wanda ba mantuwaba kuma ba makaraba yabari da gangan har alfijir yaketo to yayi asararsa kawai,
Kuma ana iyayin wutiri raka'a 5 ko 3 ko 1 yadda yazo a Hadisin ABU AYYUBAL ANSARY,
ALLAHU A'ALAM*via : Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽*
15/Al-Muharram/1441
15/September/2019
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: