*006 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SU WANE NE SUKA FI RUWAITO HADISAI DAGA CIKIN SAHABBAI?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Su wane ne sukafi rawaito hadisai a cikin sahabbai?
AMSA:
Wa’ailaikumus Salam, waɗanda suka fi ruwaito hadisai a cikin Sahabban Manzon Allah s.a.w. su ne kamar haka:
1. Abu Huraira: Shi ne ya fi duk wani sahabi yawan ruwaito hadisan Annabi s.a.w.
2. Abdullahi ɗan Umar ɗan Khaɗɗab.
3. Uwar Muminai A'isha.
4. Jabir ɗan Abdullahi.
5. Anas ɗan Malik.
6. Abdullahi ɗan Abbas.
7. Abu Sa'id Alkhudriy.
Waɗannan su ne malaman hadisi guda bakwai waɗanda suka fi sauran Sahabbai yawan ruwaito hadisan Annabi Muhammad s.a.w. Allah ya qara masu yarda baki ɗaya.
Allah ne mafi sani.*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
3/4/1440 H.
10/12/2018 M.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Storie brevi*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: