MIƘEWAN ƊALIBAI DON GAI DA MALAMAI*

143 1 0
                                    

*Tambaya ta 001:*

*MIƘEWAN ƊALIBAI DON GAI DA MALAMAI*

_Assalamu Alaikum,_

Malam ina muku sannu da qoqari, malam ina da tambaya cikin rubutunku da kuka yi game da *Martanin Mauludi* , kun kawo wani hadithi:

*مَنْ أَحَبَّ أَنْ يَتَمَثَّلَ لَهُ النَّاسُ قِيَاماً فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ*
*Duk wanda ke son mutane su miƙe masa a tsaye, to ya nemi mazauninsa a cikin Wuta.*

Malam, na kasance malamar makartar boko, idan ɗalibai za su gaishe ni sai sun yi tsaye, to kenan na shiga cikin wanan hadithin ????

*AMSA A001*

_W alkm slm w rhmt laah._

1. Da farko ba za a ce kin shiga cikin Hadisin ba kai-tsaye, domin ai hadisin cewa ya yi: *'Duk wanda yake so...'*

Don haka, idan dai ba kina so, ko kina sha'awar miƙewar yaran ba ne, ba za a ce kin shiga cikin Hadisin ba, _in shaa'al laah._

2. Amma duk da haka, abin da ya wajaba gare ki da sauran malamai irinki shi ne: Ku hana ɗalibanku miƙewar, domin koya musu kyakkyawar ɗabi'a tun suna ƙanana, kuma da toshe kafar yaɗuwar sharri a cikin al'umma. Haka maruwaicin hadisin ya yi:

3. Asalin Hadisin, Sahabi Mai Daraja ne Mu'awiyah Bn Abi-Sufyaan _(Radiyal Laahu Anhu)_ ya shiga wani daki wanda a cikinsa ya tarar da Abdullaah Bn Az-Zubair da Abdullaah Bn Amir. Sai Ibn Amir ya miƙe domin shi, shi kuwa Ibn Az-Zubair ya tabbata a zaune, bai miƙe masa ba.
Daga nan ne sai Mu'awiyah ya ce:

*اجْلِسْ يَا ابْنَ عَامِرٍ! فَإِنّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ (صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ) يَقُولُ...*
*Zauna, Ibn Amir! Domin na ji Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cewa: ...*

Sai ya ambaci Hadisin.

4. A kan haka ne As-Shaikh Al-Albaaniy _(Rahimahul Laah)_ a cikin *(Silsilah Saheehah: 1/696)* inda yake fitar da fiqhun hadisin ya ce:

Wannan hadisin ya nuna mana abubuwa guda biyu:

*Na-ɗaya:* Haram ne ga wanda ya shigo wuri ya yi sha'awar mutanen da ya tarar su miƙe ma sa.

*Na-biyu:* Wanda ya shigo kuma aka miƙe masa, sai lallai ya ƙyamaci hakan ga mutanen da suka yi masa hakan (watau ya hana su), duk kuwa da kasancewar ba ya son miƙewar. Wannan a babin: Umarni da kyakkyawa da Hana mummunan aiki ne, kuma domin toshe dukkan ƙofar sharri... Haka maruwaicin Hadisin Mu'awiyah _(Radiyal Laahu Anhu)_ shi da kansa ya nuna mana...

5. Amma abin da waɗansu suka yi na kafa hujja da misalin Hadisin da ya ce:

*قُومُوا إِلَى سَيِّدِكُمْ*
*Ku miƙe zuwa ga shugabanku*

Malaman Sunnah sun ce: Wannan ba hujja ce mai ƙarfi ba, saboda dalilai kamar haka:

A larabci: *'Qaama Lahu'* ya sha bamban da ' *Qaama Ilaihi.'*
A lokacin da na-farko ke nuna ya miƙe ne, kuma ya tsaya a matsayinsa don girmama shi, na-biyun nuni yake ga cewa, ya miƙe ne tsaye kuma ya taka zuwa gare shi domin taimaka masa, ko don wani abu dai, misali.

Shi ya sa wannan hadisin da suka jawo ya zo da ƙarin bayani a ƙarshensa mai nuna manufarsa, Watau cewa:
*فَأَنْزِلُوهُ*
*Ku sauke shi*

Malaman Hadisi da Tarihi sun san cewa wannan maganar ta auku ne a lokacin da aka kira Sahabi Sa'ad _(Radiyal Laahu Anhu)_ da ba shi da lafiya don ya yanke hukunci a kan Yahudawa. Da ya zo a kan abin hawarsa shi ne Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya faɗa wa Lansarawa:

*قُومُوا إِلَى سَيِّدِكُمْ ، فَأَنْزِلُوهُ*
*Ku tashi ga shugabanku, ku sauke shi.*

Wannan ya nuna ashe ba maganar tsayawa a wuri guda don girmamawa Hadisin yake yi, irin yadda ake yi wa shugabanni a yau ba.

A taƙaice dai, ba daidai ba ne a riƙa miƙewa tsaye don girmama wani mutum, saboda wannan Hadisin Sahihi.

Amma kuma kowane mutum yana aiki da abin da ya sani na Ilimi ne, da gwargwadon ikonsa da kuma yanayi ko halin da yake ciki.

Allaah Ta'aala ya ce:

*فَاتَّقُوا اللهَ مَااسْتَطَعْتُمْ*
*Ku bi Allaah da taqawa da gwargwadon iyawarku.*

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*

_Wal Laahu A'lam_ .
19 - 12 - 2017

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now