*183 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*NA CI ABINCI DAI-DAI LOKACIN KETOWAR ALFIJIR, YA MATSAYIN AZUMINA?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum mallam, Ina mura Na sha magani kuma Ina da niyyan daukar azumi, sakamakon maganin I wake up late 5:00 daidai na falka, sai na yi amfani da 5 minites na ci abinci, wato 5:05 kenan mallam ya matsayin azumina?
AMSA:
Wa'alaikumus Salam, ƴar uwa matuqar lokacin da mutum ya ci abincin sahur Alfijir na gaskiya ya keto ko da da minti ɗaya ne, to ba shi da azumi, sai ya rama wannan azumin. Amma idan dai-dai qarfe biyar ɗin nan Alfijir na gaskiya bai riga ya keto ba, to azuminki ya inganta, in kuwa Alfijir na gaskiya ya riga ya bayyana ko da kuwa da minti ɗaya ne, to lallai ba ki da azumin wannan yinin.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu zarewa*
15/11/1440 h.
18/07/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Historia Corta*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: