*YA MATSAYIN SHIGA BANDAKI DA WAYA MAI ALQUR'ANI

99 1 0
                                    

*025 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA MATSAYIN SHIGA BANDAKI DA WAYA MAI ALQUR’ANI?*

TAMBAYA:

Assalamu Alaikum. Malam ni ce wata tana da compiled Qur'an shin zan iya shiga bayi da ita domin haska fitilar wayata?

AMSA:

Game da shiga banɗaki da waya (handset) mai qunshe da Alqur'ani a ciki, malaman Musulunci sun bayar da fatawowi a kai, musamman ma na zamanin da muke ciki, wanda a ciki ne aka sami wayar salula mai ɗauke da Alqur'ani.

Kai tsaye dai shiga bayi da Alqur'ani haramun ne sai idan akwai lalura mai girma. Hadisin da Anas Allah ya qara masa yarda ya ruwaito, wanda yake cewa "Annabi s.a.w idan zai shiga bayi yana cire zobensa" ya yi nuni a kan haka, domin an ce rubutun da ke kan zoben shi ne "MUHAMMADUR RASULILLAH" (محمد الرسول الله), wanda kuma wannan wani ɓangare ne na wata aya a Alqur'ani.
Abu Dawud 19, Tirmizhi 1746, Nasa'i 178, Ibn Majah 303.

Amma kuma idan mutum yana jin tsoron in ya ajiye Alqur'aninsa a waje ya shiga bayi za a iya sace masa, wasu malaman sun ce ba laifi idan ya shiga da shi bisa wannan lalurar, kamar yadda Sheikh Ibn Baaz ya bayyana a Majmu'u Fatawa.
Duba Majmu'u Fataawa na Ibn Baáz (10/30).

Amma kuma idan Alqur'anin yana cikin salula ne ba laifi idan an shiga da salula ɗin, sai dai an karhanta (qyamaci) a buɗe Alqur'anin wayar salular a cikin bayi, ko kuma idan ya kasance akwai rubutun Alqur'ani a jikin screen ɗin wayar, shi ma wannan an karhanta shiga da shi bayi, domin shi ma kamar wanda ke kan zoben can ne, wato kenan idan a cikin wayar ba buɗe Alqur'anin aka yi ba babu laifi.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
27/4/1440 h.
03/01/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now