*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*HUKUNCIN YIN FITSARI A TSAYE*
TAMBAYA:
Assalamu Alaikum malam. meye hukuncin me fitsari a tsaye?
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu, ba a haramta yin fitsari a tsaye ba, sai dai an sunnanta yin sa a tsugunne, saboda maganar Nana A'isha Allah ya qara mata yarda da take cewa: "Duk wanda ya ba ku labarin cewa Annabi ﷺ yana yin fitsari a tsaye kada ku gaskata shi, bai kasance yana yin fitsari ba face sai a tsugunne". Tirmizhiy ya ruwaito a hadisi mai lamba ta 12. Kuma ya ce: Wannan hadisin shi ne abin da ya fi inganci a wannan babin.
Amma kuma duk da wannan hadisi na Nana A'isha, an ruwaito rangwame game da yin fitsari a tsaye, amma da sharaɗin idan an aminta daga tartsatsin fitsarin a jiki da tufafi, kuma ya zamana mutum ya aminta daga bayyanar da al'aurarsa ga jama'a, Huzaifa Allah ya qara masa yarda ya ce: "Manzon Allah ﷺ ya zo wajen zubar da shara na waɗansu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye, ya sa a kawo masa ruwa, sai na zo masa da ruwan, sai ya yi alwala". Bukhariy 224. Muslim 273.
Babu cin karo a tsakamin hadisin Nana A'isha da wannan hadisi na Huzaifa Allah ya qara masu yarda, domin wannan hadisin zai iya zama Annabi ﷺ ya aikata hakan ne saboda ba waje ne da zai yiwu masa ya tsugunna ba, ko kuma ya zama ya aikata hakan ne don ya nuna wa mutane cewa yin fitsari a tsaye ba haramun ba ne, sai dai kuma hakan ba ya kore cewa asalin yadda lamarin yake shi ne yadda Nana A'isha ta ambata cewa Annabi ﷺ yana yin fitsari ne a taugunne, wato hakan sunnah ce amma kuma ba ya haramta akasinsa.
Sai dai yana da kyau mutum ya kaucewa yin duk wani abu a idon jama'a da zai iya sa gamagarin mutane su riqa ganinsa a matsayin mai saɓo ko maras tarbiyya da abin da ya yi kama da hakan, sai dai in ya zama dole sai ya aikata.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
17/6/1440 h.
22/02/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: