*SHIN AKWAI WASU KEƁUN SURORI DA AKE KARANTAWA A SALLAR WALHA

1K 0 0
                                    

*065 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN AKWAI WASU KEƁUN SURORI DA AKE KARANTAWA A SALLAR WALHA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum Malam tambayata ita ce, ina yin walaha ina karanta kowacce surah amma sai aka ce min raka'a ta biyu suratul Naba'i zan riqa karantawa, shi ne nake tambaya malam?

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, ƴar uwa yadda kike yi a farkon nan shi ne ya fi zama daidai, wato ki riqa karanta duk surar da ta sauqaqa a gare ki a dukkan raka'o'in, domin hakan shi ne asali, kuma shi ke da dalilai bayyanannu a iya abin da na sani.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
07/6/1440 h.
12/02/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now