*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*MENE NE HUKUNCIN WANDA YANA AZKAR YANA WASAN GAME?*
TAMBAYA:
Assalamu Alaikum, malam dan Allah ya hukuncin meyin Azkar yana game?
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu, Mafificin zikiri shi ne wanda aka yi shi da harshe tare da halarto da zuciya a lokacin yin sa, kamar yadda kuma mafi raunin zikiri shi ne wanda aka yi shi da harshe kaɗai, kamar yadda Imamun Nawawiy ya kawo magangnun Malam Alqali Iyadh masu kyau a kan haka.
Duba Sharhu Sahihi Muslim 9/16-17.Mai yin game a lokacin da yake zikiri ba zai yiwu masa ya iya halarto da zuciyarsa ga abin da harshensa ke faɗi ba, saboda ba wani mutum da Allah ya sa masa zuciya guda biyu a cikinsa, ballantana ya ce zai iya raba zuciyar nan wuri biyu ɗaya na ga zikirin da yake yi, ɗayar kuma tana ga wasan game ɗin da yake yi, don haka haɗa zikiri da wasan game bai dace ba, kuma babu kamala a cikin wannan zikiri, kamar yadda har wani alaramma na wuce a makon da ya gabata shi ma yana tilawa kuma yana game a wayarsa, haɗa duka waɗannan abubuwa a lokaci guda bai dace ba.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
29/6/1440 h.
06/03/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: