*TAMBAYA TA 087*
*MIJINTA YA RASU… TA TAFI UMRAH*
_As-Salamu Alaikum,_
Don Allaah, menene hukuncin matar da mijinta ya rasu, ranar kwana na takwas ta tafi umrah?
*AMSA A087*
_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah._
Kamar yadda ya gabata a cikin amsar tambaya ta A083, mai takaba tana zama a cikin gidanta ne a cikin halin da ba na kwalliya ko ado ba, har sai ta yi watanni huɗu da kwanaki goma, daga ranar da mijinta ya rasu.
Haka kuma kamar yadda muka faɗa a cikin amsar tambaya ra A005, wadda ta ke cikin idda ko takaba tana iya fita daga gidanta da rana, idan larurar fitar ta kama ta. Saboda hadisin da Al-Imaam Muslim ya riwaito a cikin sahih (Lamba: 1483) daga Jaabir Bn Abdillaah _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ ya ce:
An saki innata, sai ta yi nufi ta je ta yanke 'ya'yan itacen dabinonta, sai wani mutum ya hana ta. Sai ta tafi ta gaya wa Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ sai ya ce:
بَلَى فَجُدِّي نَخْلَكِ ، فَإِنَّكِ عَسَى أَنْ تَصَّدَّقِي ، أَوْ تَفْعَلِي مَعْرُوفاً
A'a, ki je ki yanko 'ya'yan dabinonki, domin za ki iya yin sadaka, ko kuma ki yi wani aikin alkhairi.Sai dai kuma wannan bai haɗa da yin doguwar tafiya gari-ya-gari ba, kamar zuwa Hajji ko Umrah. Haka manyan malamai suka ce:
‘Kuma mace ba za ta fita zuwa hajji a cikin iddar mutuwar miji ba. Amma za ta iya fita idan iddar saki na-karshe ne, watau wanda babu kome a cikinsa. Idan kuwa sakin da ya ke akwai kome ne, to ita mace a cikin iddar tana zaune a gidan mijinta ne a matsayin mai neman aure, kuma ita kamar matar aure ce. (Don haka ba za ta fita zuwa Hajji ba).
Sannan idan mace ta fita zuwa Hajji ko Umrah sai ta samu labarin mijinta ya rasu, to sai ta dawo ta yi idda a ɗakinta idan dai ba ta yi nisa da tafiyar ba. _(Ibn Qudaamah (Rahimahul Laah) ya faɗi hakan a cikin Al-Mughnee: 3/240-241)._Ya tabbata daga Khalifah Umar Bn Al-Khattaab Ameer Al-Mu’mineen cewa:
Ya mayar da matan da suka fita Hajji ko Umrah a cikin Iddodinsu. _(Ibn Abi-Shaibah: 3/326)._
Wannan ya nuna macen da mijinta ta rasu bai halatta ta fita zuwa Hajji ko Umrah ba har sai ta gama iddarta, na tsawon watanni hudu da kwanaki goma.
Sai dai ko in ya rasu a lokacin tana da ciki ne, kuma ta haihu a bayan rasuwarsa. Domin kamar yadda muka ji a amsar tambaya ta 083, irin wannan matar tana gama idda ne a lokacin da ta haihu.
_Wal Laahu A’lam._
_3/5/2019_
_6: 54pm_*sheikh Muhammad Abdullah Assalafy*
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: