*YA HUKUNCIN SHAFA MAI A BAKI GA MAI AZUMI?*

174 1 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA HUKUNCIN SHAFA MAI A BAKI GA MAI AZUMI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, Allah ya saka ma malam da alheri, malam dan allah ya halasta mutum yana azumi ya sa mai na baki, wato wet lips saboda bushewar baki? Nagode.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, ƴar uwa babu laifi idan mutumin da ke azumi ya shafa mai a leɓensa saboda kawar da bushewar laɓɓan, amma ya wajaba ya tofar da shi a duk lokacin da ya ji alamarsa a bakinsa, kada ya bar shi ya gangara maqoshinsa. Amma idan aka yi rashin sa'a ya gangara cikinsa ba da nufi ba, to babu laifi, kamar yadda idan yana alwala sai ruwa ya kuɓuce masa ya isa cikinsa ba da nufi ba azumin sa bai ɓaci ba.

Duba Majmú'u Fataáwá na Ibn Uthaimeen 19/224.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
26/8/1440 h.
02/05/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now