SHIN ANA JANYE SAKI BAYAN AN YI SHI?*

154 3 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN ANA JANYE SAKI BAYAN AN YI SHI?*

TAMBAYA:

Assalamu Alaikum, malam miji ne ya saki matarsa saki 1 a ranar ya janye bayan an daidaita, sai mahaifiyarsa ta zo gidan ana maida magana sai ya ce dama na sake ki na sakeki kitafi gidanku, malan ya sakin yake?

AMSA:

Wa'alaikumus Salam, ai ba a janye saki bayan an yi shi, matuqar mutum ya ce ya saki matarsa, to saki ya tabbata, ba maganar ya ce ya janye ko ya fasa, sai dai ki ce an sulhunta an ci gaba da zama a kan wannan saki da aka yi. Sannan hukuncin saki ɗayan nan ne za a yi masa hukunci a kai, saboda ai labarin abin da ya wuce yake bayarwa a lokacin mayar da magana, yana cikin magana ne sai ya ce dama ai na sake ki, wato sakin nan da ya gabatar yake ba da labari, sai kuma ya ce na sake ki ki tafi gidanku, wannan a gaskiya a zahiri sakin da ya gabatar yake tabbatarwa ba wani sabo ba.

Sai dai yana da kyau bayan ya dawo hayyacinsa a tuntuɓe shi a kan hakan don a ji abin da yake nufi, shin sakin da ya riga ya gabatar yake nufi tare da wani qarin sakin, ko kuwa sakin da ya riga ya gabatar ne kaɗai yake qara tabbatarwa? saboda inda shubhar take a maganarsa da ya ce: "dama na sake ki", wato labari ne wannan yake bayarwa tare da tabbatar da abin da ya wuce.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
18/6/1440 h.
23/02/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now