*017 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*HUKUNCIN SHAFA A KAN KHUFFI DA SAFA*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Dan Allah ina son in san hukunci game da shafa a kan huffi ko safa, idan mutum ya yi alwala kuma ya saka safa to idan har fitsari ya kama shi, shin idan ya je ya yi, shin idan har zai yi alwala sai ya sake cire safar ko kuma zai yi shafa a kanta? Na gode.
AMSA:
Shafa a kan khuffi ko safa sunnah ce ba farilla ba. Ya halasta idan mutum ya saka khuffinsa ko safarsa a lokacin da yake da tsarki, yayin da ya zo yin alwala ba sai ya cire khuffin ko safar ba, kawai sai ya yi shafa a kansu.
Haka nan idan alwalar mutum ta karye akwai khuffi ko safa a qafarsa, idan ya yi nufin sake yin alwala ba dole sai ya cire su ba, kawai sai ya yi shafa a kansu, dalilai da yawa sun zo a kan haka a hadisan Annabi s.a.w ingantattu, daga ciki akwai hadisin da Sahabin Annabi s.a.w Almugeeratu ɗan Shu'uba Allah ya qara masa yarda ya ruwaito, a inda yake cewa:
“Na kasance tare da Annabi s.a.w. a halin tafiya, sai na yi nufin in cire masa khuffinsa, sai Annabi s.a.w ya ce mini "KA BAR SU, DOMIN NI NA SA SU SUNA DA TSARKI", Annabi s.a.w da ya gama alwala sai ya yi shafa a kansu”.
Bukhari 203, Muslim 274.Baya ga wannan akwai hadisai da dama da Sahabbai suka ruwaito cewa Annabi s.a.w idan ya saka khuffi a halin tsarki, yayin da zai sake yin alwala ba ya cire su don wanke qafa, barin su kawai yake yi, sai ya yi shafa a kansu.
A'immatul fuqaha'i sun haɗu a kan halascin yin shafa a kan khuffi ko safa a lokacin alwala matuqar lokacin da aka sa su an sa su ne a halin tsarki. Inda kawai suka yi saɓani shi ne adadin kwanakin da mutum zai iya yi yana shafa a kan khuffi ko safar.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
16/4/1440 h.
23/12/2018 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: